Ministar kuɗi ta nemi a yi bincike mai zurfi

Hakkin mallakar hoto hausa
Image caption Ngozi Okonjo-Iweala, ministar kuɗin Nijeriya

Ministar kudi ta Nijeriya, Ngozi Okonjo-Iweala tace, za ta so ganin masu bincike masu zaman kansu daga waje sun duba zargin salwantar dalar Amurka biliyan 20 da ya kamata a ce sun shiga asusun gwamnatin kasar.

A wata sanarwa da wakilin BBC kan tattalin arziki Robert Peston ya samu, ministar wacce take kula tattalin arzikin kasar ta kuma ce, tun farko dai matsayinta shi ne, a yi bincike mai zaman kansa akan ɓatan kudin.

Ngozi Okonjo Iweala ta kuma kara da cewa, tunda shugaba Goodluck Jonathan ya ce, ofishin babban mai binciken kudi na gwamnatin tarayya zai yi bincike a kan salwantar kudaden, tana fatan ganin gaskiya ta bayyana.

Ta kuma ce, tana son ganin ofishin babban mai binciken ƙudi na tarayya ya gaggauta sa masu bincike daga waje su duba batun.

Wasu sun ce, dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi na da alaƙa da tonon sililin da ya yi dagane da batan kudin dalar Amurka biliyan ashirin.

Amma gwamnati ta ce, ta dakatar da shi ne saboda zarginsa da aikata ba daidai ba wajen gudanar da kudaden babban bankin tarayya wato CBN.