Rooney: Mu 'yan wasa ne keda laifi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rooney ya sake sanya hannun kwanturagin shekaru biyar da rabi

Dan wasan gaban Manchester United Wayne Rooney ya ce dole ne shi da ‘yan uwansa ‘yan wasa su dauki alhakin matsayin kulab din a gasar Premier League.

Zakarun na United suna matsayi ne na shida a yanzu kuma Chelsea ta dara su da maki 15.

Rooney ya ce a matsayin mu na ‘yan wasa dole ne mu dauki alhakin matsayin da muke a gasar Premier.

Rooney dai ya sake sanya hannun kwanturagi da Manchester United na shekaru biyar da rabi a makon daya gabata