'Nijeriya ma ta na fama da ƙarancin ungozomomi'

Hakkin mallakar hoto Mike Goldwater World Vision

Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta ce, Nijeriya na daga cikin kasashen da jarirai da ba a jima da haihuwa ba da dama ke mutuwa saboda ƙarancin unguzomomi.

Kungiyar ta ce, kowacce shekara jariria da ba a jima da haihuwa ba miliyan guda ne ke mutuwa.

Save the Children ta ce, lamarin ya fi tsananta ne a kasashen da suka hada da Nijeriya, da Pakistan da kuma Saliyo.

Kungiyar agajin ta kuma ce, kashe karin dalar Amurka biyar ga harkar kiwon lafiya domin kowanne mutum guda zai taimaka wajen horar da ungozomomi.