Masar: An yankewa mutane 26 hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Dole sai wani babban jami'in musulunci ya tabbatar da hukuncin.

Wata kotu a Masar ta yanke wa wasu mutane 26 hukuncin kisa, bayan ta same su da laifin kafa wata kungiya ta 'yan ta'adda, wadda ta shirya kai hare-hare a kan jiragen ruwan da ke bi ta mashigin Suez.

An kuma sami mutanen da laifin kera makamai masu linzami da bama-bamai, da kuma tunzura jama'a su kai hari a kan 'yan sanda, da sojoji da kuma mabiya addinin Krista.

An yi wa mutanen 26 shari'ar ce a bayan idonsu.

A yanzu dole sai wani babban jami'in musulunci ya tabbatar da hukuncin.

A 'yan watannin nan dai, Masar ta sha fama da hare-hare daga wadanda ake zaton masu tsatsauran ra'ayin Musulunci ne.