'Hezbollah zata kaiwa Isra'ila hari'

Hakkin mallakar hoto d
Image caption Hezbollah tace zata zabi lokaci da wurin da zata maida martani.

Kungiyar Hezbollah tace za ta maida martani ga wani hari da Isra'ila ta kai mata ta sama tunda farkon wannan makon akan daya daga cikin sansanoninta dake kan iyakar Lebanon da Isra'ilar.

Kungiyar ta bayyana harin da cewa wani cin mutunci ne akan 'yancin kan kasar Lebanon.

Hezbollah tace zata zabi lokaci da kuma wuri da kuma hanya mafi dacewa na maida martani ga harin.

Israel dai bata bada tabbaci a hukumance cewa ita ta kai wannan hari ba.

Amma a wani taron manema labaru a ranar Talata, Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce gwamnatinsa zata yi duk wani abu da ya zama wajibi na kare tsaron lafiyar al'ummar Isra'ila