Buni Yadi: Amurka ta nuna damuwa

Hakkin mallakar hoto

Gwamnatin Amurka ta nuna rashin jin dadinta dangane da yadda rundunar sojojin Nigeriar ke tunkarar hallaka jama'a da 'yan Boko Haram suke yi a arewa maso gabashin ƙasar.

Mataimakiyar Sakataren harkokin waje mai kula da harkokin Africa ta gwamnatin Amurkar, Bisa Williams ta shaidawa BBC cewar Amurka ta damu matuƙa a kan yadda ake tunkarar rikicin.

Bisa Williams ta ce, tuni shaidawa shugaba Jonathan rashin jin dadinta dangen da lamarin.

Amurka ta kuma ce, kungiyar Boko Haram ta zama wata babbar barazana, musamman ga al'ummar arewacin Nijeriya.

Hari na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai kwalejin gwamnatin tarayya a Buni Yadi inda aka hallaka dalibai 29.