Cuta ta kashe 'yan makaranta a Kebbi

Gwamna Sa'idu Dakingari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daliban na fama ne da matsancin ciwo kai da ciwon ciki da kuma zazzabi

Jami'an lafiya a jihar Kebbin arewacin Nigeria na gudanar da bincike domin gano nau'in wata bakuwar cuta data barke a wata makaranta da ke jahar wadda yanzu haka ta hallaka dalibai hudu.

Haka kuma cutar wadda ta hada da tsananin zafin Jiki ta kwantar da wasu daliban 55 a asibiti.

Jami'an babban asibitin garin Argungu inda aka kwantar da daliban na kwalejin Kanta da ke garin sun shaida wa BBC cewa sun karbi dalibai 55 da suka kamu da cutar tun daga ranar asabar.

Daliban dai na fama ne da matsanancin ciwo kai da ciwon ciki da kuma zazzabi mai tsanani

Kwamishinan lafiya na jahar Alhaji Shehu Aliyu Sambawa ya shaidawa BBC cewa suna ci gaba da kokarin gano kowace irin cuta ce wadda aka danganta da bugun aljani.