"Kar Amurka ta sayar wa Iraq makamai"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanata John McCain na zargin Iraq na cinikin makamai da Iran.

Dan majalisar dattawan Amurka, John McCain, ya bukaci a dakatar da wani cinikin jiragen soji masu saukar ungulu samfurin Apache guda 24 da Amurka ta sayar wa Iraq har sai an tantance zargin cewa gwamnatin Iraq ta kulla yarjejeniyar cinikin makamai da Iran.

Kakakin Fadar White House, Jay Carney ya ce gwamnatin Iraq ta musanta rahoton da kafafen yada labarai su ka fitar ranar Talata cewa za ta sayi makaman kusa $200 miliyan daga Iran.

Hakan dai ya saba wa takunkumin da Amurka da majalisar dinkin duniya suka kakabawa Iran.

Wasu daga cikin manyan 'yan siyasar Iran ciki har da mataimakin Pirai minista sun bayyana bacin ransu da rahotannin gwamnatin Iraq da ke karkashin jagorancin 'yan shi'a ta kulla cinikin makamai da Iran a asirce.