Nigeria: Mafarauta na fuskantar barazana

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mafarautan arewacin Nigeria sun koka

Rahotanni sun bayanna cewa mafarauta da kanyi takakkiya daga arewacin Nigeria zuwa kudanci domin yin farauta na cin karo da matsaloli.

Shugaban 'yan arewa mazauna jahar Edo a kudancin Nigeria Alhaji Badamasi Saleh ya shaidawa BBC cewa makonni uku da suka wuce jami'an tsaron jahar Edo sun kama wasu mafarauta su 10 da suka taso daga jahar Niger a arewacin kasar bayan an zarge su da cewa 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne.

Shugaban ya yi kira da mafarautan su dakatar da shiga kudancin kasar saboda wannan barazana da ake masu.

Tun shekaru da dama idan rani ya yi, mafarauta daga arewacin Nigeria sukan yi shiri su nufi dazuzukan dake kudancin kasar tare da makamansu na harbi domin gudanar da sana'arsu ta farautar namun daji.