Uganda za ta kare lafiyar 'yan luwadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sabuwar dokar ta tanadi daurin rai da rai ga masu luwadi da madigo a Uganda.

Mahukuntan Uganda sun ba da tabbacin cewa ba za a nuna wa masu luwadi da madigo wariya ba a duk lokacin da suka bukaci kiwon lafiya, duk da zartar da sabuwar dokar yaki da wannan dabi'ar cikin makon nan.

Ministan lafiya, Dr Ru-hakana Rugunda ya shaida wa BBC cewa dukkan mutane - walau masu luwadi da madigo ko akasin haka - za su samu cikakkiyar kulawa kuma wajibi ne jami'an lafiya su tabbatar da ka'idar aikinsu ta boye sirrin mara sa lafiya.

Ya kuma shawarci al'ummar kasar da su baiyana wa likitocinsu gaskiyar cututtukan da ke damunsu.

Kungiyoyin yaki da cutar AIDS dai sun yi gargadin cewa sabuwar dokar da ta tsananta hukuncin da za a iya yi wa masu luwadi da madigo za ta yi mummunan tasiri kan kokarin da Uganda ke yi na yaki da yaduwar cutar a fadin kasar.

Karin bayani