Amurka na kokwanton taimakawa Uganda

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka na tallafawa Uganda ta fuskar yaki da cutar HIV AIDS

Jakadan Amurka a Kampala Scott Delisi ya shaidawa BBC cewa yana bukatar karin haske game da dokar hana yin luwadin Uganda kafin Amurka ta yanke hukuncin ko zata ci gaba da shirin tallafawa Kasar musamman akan cutar HIV AIDS.

Mr. Delisi ya ce yana bukatar tabbaci cewa ma'aikatan Amurkar da kuma kawayen ta ba zasu fuskanci hatsarin daurin gidan yari ba.

Jakadan ya kuma soki jaridar Uganda saboda wallafa jerin sunayen abinda ta kira manyan 'yan luwadin Kasar.

Tun farko dai Shugaba Obama na Amurka ya yi gargadin cewa dangantakar Amurka da Uganda zata lalace idan har gwamnatin Ugandan ta sanya hannu kan dokar hana yin luwadin.