Shafin Weibo na China ya samu riba

Hakkin mallakar hoto Reuters

Riba ta ƙaru sosai ga kamfanin nan na fadi son ka dake da salon Twitter a China wato Wiebo, saboda ƙaruwar talla da shafin yake samu.

Kamfanin ya ce, ribar dalar Amurka miliyan 44 tsakanin watannin Oktoba da Disambar bara.

China dai ita ce babbar kasuwar hada-hadar Intanet, kuma shafukan sada zumunta sun samu karbuwa sosai a kasar.

Kamfanin ya sanar da samun wannan riba a daidai lokacin da yake shirin zuwa kasuwar hannayen jari a Amurka domin samun karin jarin dalar Amurka miliyan 500.

Shafin sada zumuntar na Weibo ya ce, masu amfani da shi sun kai mutane miliyan 500.

China ita ce, babbar kasuwar hada-hadar Intanet, kuma shafukan sada zumunta suna da farin jini a kasar.

Dan haka ne ma kamfanoni da dama suke tallata hajarsu a shafin na Weibo domin samun kasuwa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ƙalubale

Alkaluma na nuna cewa, kudin shiga da shafin Weibo yake samu daga tallace-tallace na karuwa sosai.

Sai dai kuma wasu alkaluman na nuna cewa, koda a bara mutane miliyan 28 ne suka daina amfani da shafin na Weibo.

Wannan dai shi ne karon farko da shafin ya samu koma baya tun bayan gwamnati ta kaddamar da yaki da wadanda ta kira masu yada jita-jita.

Shafin Wiebo dai ya yi fice ne saboda baiwa jama'a damar fadin ra'ayinsu, amma hakan ta sa gwamnati ta dau mataki domin dakile bayyana ra'ayoyi a shafukan Intanet.

China ta kaddamar da wata doka ta hukunta masu amfani da shafuka dake da salon irin na Twitter, kuma har an kama wasu da dama.

Kamfanin na Weibo ya ce, wannan shekarar zai maida hankali ne ga jawo hankalin masu amfani da kafar sadarwa ta Intanet.