Michika da Shuwa: An kashe mutane 28

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni na cewa, yawan mutanen da aka kashe a garin Michika da Shuwa dake jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Nijeriya kai aƙalla mutane 28.

Wani mazaunin ƙauyen Shuwa ya shaidawa BBC sun ƙirga gawar mutane 24, kuma wasu da dama sun jikkata.

A garin Michika wasu shaidu sun ce, sun ga gawar mutane uku.

Harin dai ya firgita mutane da dama da suka bazama cikin daji domin tsira.

Mutane da dama daga garin Michika sun kwana ne a cikin daji da kuma kan duwatsu.