Ana zaman ɗar-ɗar a Michika

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Sassan arewa maso gabas suna fama da hare-hare

Bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai garin Michika dake jihar Adamawa, yanzu haka ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a garin.

Yayin harin wanda aka kai irin sa a kauyen Shuwa da ke karamar hukumar Madagali an ƙona bankuna, da ofishin 'yan sanda da kuma shaguna da dama dake bakin titi.

Wasu shaidu sun ce, sun ga gawar mutane uku.

Harin dai ya firgita mutane da dama da suka bazama cikin daji domin tsira.

Mutane da dama sun kwana ne a cikin daji da kuma kan duwatsu.

A kauyen Shuwa dake karamar hukumar Madagali an kai wani harin.