Nijeriya: An yi wa alƙalai 2 ritayar dole

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Babbar kotun ɗaukaka ƙara ta Nijeriya

Hukumar da ke sa ido akan harkokin shari'a a Nijeriya ta yiwa wasu alƙalan kotunan tarayya biyu ritayar dole bayan bincike ya same su da laifuka da dama na aikata ba daidai ba.

A wani zama da hukumar ta yi ƙarƙashin jagorancin babbar mai shari'a ta Nijeriya, Aloma Mariam Mukhtar, an kuma dakatar da alƙalan biyu nan take.

Wata sanarwa mai da aka fitar yau mai sa hannun muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na hukumar, Soji Oye ta ce, an samu alƙalan biyu ne da laifuka da dama.

An sami mai shari'a G.K. Olotu da laifukan da suka hada da jinkirta bada hukunci a wata shari'a har fiye da kwanaki casa'in.

An kuma sami mai shari'a U. A. Inyang da laifin ƙin bari a shigar da bayanan wani shaida a wata shari'a da gangan.

Laifukan da aka samu alƙalan biyu da aikatawa sun hada da ƙin yanke hukunci da gangan a wasu shari'u duk da cewar an gabatar da dukkan bayanai.

Hukumar sa ido akan bangaren shari'ar kuma ta yi kashedi ga shugaban kutun ɗaukaka ƙara shiyyar Kaduna mai shari'a Dalhatu wanda shi ne shugaban kotun.

Ana dai zarginsa ne da yin sakaci da aiki.

Wasu a Nijeriya sun sha kokawa da abinda suka kira rashin ɗa'a dake karuwa a bangaren shari'ar kasar.