Sabuwar gwamnatin Ukraine

Prime Minstan Ukraine na wucin gadi Arseniy Yatsenyuk Hakkin mallakar hoto .
Image caption Sabuwar gwamnatin Ukraine za ta fuskanci kalubalen farfado da tattalin arzikin kasar da ya durkushe.

An gabatar da shugabannin 'yan adawa da suka jagoranci zanga-zanga a Ukraine da ta hambarar da shugaba Viktor Yanukovych a dandalin 'yanci, ana sa ran za a ba wani shugaban 'yan adawa Arseniy Yatsenyuk prime ministan kasar.

A wata tattaunawa da BBC Mr Yatsenyuk yace kasar sa na cikin bala'i, ya kuma bayyana wadanda suka amince su shiga sabuwar gwamnati da wadanda suke shirin bata siyasar su dan za su dauki matakai dan ceto ukraine daga fadawa matsin tattalin arziki.

Ya kuma ce za su dauki matakai na ba sani ba sabo saboda cin hanci da rashawa ya mamaye gwamnatin da ta gabata, wanda ta kai kasar na cikin matsanancin rashin kudi.

Suma Ministocin da ake jin za su shiga gwamnatin wucin-gadin Ukraine, sun bayyana a gaban dimbin jama'a a dandalin 'yancin kai a Kiev babban birnin kasar.