'Babban hafsan sojin Nigeria ya tare a Maiduguri'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kashe kashe na karuwa a arewa maso gabashin Nigeria

A Nigeria, majalisar dattawan kasar ta umurci babban hafsan sojin kasar , Laftanar Janar Kenneth Minimah da ya tare shi da sauran mukarrabansa a Maiduguri don ganin an kawo karshen hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa.

Kwamitin kula da harkokin tsaro na Majalisar dattawan ya baiwa babban hafsan sojin kasar wannan umurni ne a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin don kare kasafin kudin da bangaren zartarwa ya kebewa sojojin kasar a kasafin kudin wannan shekarar.

'Yan majalisar sun nuna damuwar su game da yawan kashe kashen da ke faruwa a wannan yanki.

A baya dai gwamnan jahar Borno a Najeriyar Alhaji Kasshim Shettima ya yi zargin cewar sojojin kasar basu da isassun kayan aiki wajen yakar 'ya'yan kungiyar, sai dai gwamnatin kasar ta musanta wannan zargi.

Shi ma gwamnan jahar Yobe a Najeriyar ya bayyana takaicinsa game da gazawar sojojin kasar wajen tunkarar maharan da suka kaiwa wata kwalejin gwamnatin tarayya a jahar sa.