Somalia: Bam ya halaka mutane 12

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kungiyar Al Shabaab ta sha kai hare-hare a Mogadishu

Wani ɗan ƙunar baƙin wake da ya yi amfani da mota ya halaka mutane aƙalla goma sha biyu, kana wasu mutanen takwas suka jikkata yayin wani hari a Mogadishu babban birnin Somalia.

Lamarin ya auku ne a wajen hedikwatar hukumomin tsaron ƙasar.

Wakilin BBC a birnin ya ce, uku daga cikin waɗanda harin ya halaka jami'an tsaro ne, sauran kuma fararen hula ne a wani wurin cin abinci dake kusa.

Cikin 'yan makonnin nan tashin hankali ya ƙaru a birnin Mogadishu, inda ake samun arangama tsakanin jami'an tsaro da kuma 'yan ƙungiyar Al Shabaab.