Yingluck da badakalar shinkafa

Prime Ministar Thailand Yingluck Shinawatra Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Prime Ministar ta dade tana fuskanatar matsin lambar ta sauka daga mukamin ta a kasar.

Magoya bayan Prime Ministar Thailand Yingluck Shinawat sun zagaye ofishin hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa, tare da kulle babbar kofar shiga ta yadda ba mai shiga ofishin.

A yau ne ake sa ran Yingluck Shinawat ta bayyana a gaban hukumar, domin fuskantar tuhumar da ake mata na badakalar shirin tallafin shinkafa na gwamnati, sai dai ta musanta wannan zargi.

Miss Yingluck dai ta bar babban birnin kasar Bankok domin gujewa masu zanga-zanga, idan aka same ta da laifi zata iya fuskantar hukuncin tsigeta daga mukamin Prime Ministar kasar.

Wakilin BBC yace Miss Yingluck ta yi suna dalilin shirin gwamnati na tallafin shinkafa Yingluch ga miliyoyin manoman kasar.yingluck shinawat