Ba a kai wa Nyako hari ba - sojoji

Image caption Shi dai gwamnan ya ce hari aka kai wa tawagarsa

Rundunar sojin Nigeria ta ce rahotannin da ke cewa an kai wa tawagar gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, hari yayin da yake yin ziyarar jaje a Shuwa ba gaskiya ba ne.

Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar Chris Olukolade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai ranar Juma'a.

Ya ce tawagar gwamnan ta gamu da cikas ne bayan da wasu suka yi zaton mahara ne, lamarin da ya firgita su.

Shi dai kakakin gwamnan, Ahmad Sajo, ya shaida wa BBC cewa wasu mahara sun katse wa tawagarsu hanzari yayin da yake ziyartar wuraren da aka kai hari a kwanan nan, inda aka hallaka mutane kimanin talatin.

Lamarin dai ya sa gwamnan da tawagarsa suka juya suka koma gida.

Karin bayani