Burma: An zargi Likitoci da fifita musulmi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption MSF ita ce kungiyar data fi kowacce samar da harkar kiwon lafiya a yankin

Gwamnatin Burma ta dakatar da aikace aikacen daya daga cikin manyan kungiyoyin bayar da agaji ta Medicins Sans Frontieres ko kuma MSF saboda zargin tana fifita musulmi a jahar Rakhine inda ake fama da rikici.

Yayinda yake magana da BBC, wani mai magana da yawun gwamnati ya yi zargin cewa kungiyar likitoci ta Medicins Sans Frontieres ko kuma MSF tana goyan bayan musulmin Rohingya .

Kungiyar MSF ita ce kungiyar data fi kowacce samar da harkar kiwon lafiya a yankin.

Tana samar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu da kuma gudanar da shirye shirye na kawar da cutar HIV da kuma yaki da cutar zazzabin cizon sauro.

Wakilin BBC a Myanmar wanda da aka fi sani da Burma ya ce an yi tashe tashen hankula a jahar Rakhine tsakanin mabiya addinin Bhudda da kuma al'ummar Rohingya.

Karin bayani