Ghana: Gawarwakin yara 5 sun salwanta

Image caption John Mahama, shugaban Ghana

Ministar kiwon lafiya ta Ghana ta baiwa wani babban asibitin garin Kumasi wa'adin nan da kwanaki 14 ya fitar da gawarwakin yara kanana biyar da suka salwanta, saboda asibitin ya ce, barin jariran aka yi.

Tuni dai aka tuhumi mutane 7 da laifin sata da kitsa sace jarirai a asibitin koyarwa na Komfo Anokye a farkon watan Fabrairu.

Wata mai suna Suwaiba Mumuni na daga cikin iyayen da aka sace jariransu a asbitin, kuma ta fadawa BBC ta yi imanin har yanzu jaririnta yana da rai.

Batun salwantar jariran ya harzuka mutane a birnin Accra.

Matasa da suka harzuka sun aukawa asibitin a Kumasi, lamarin ya sa an rufe sashen haihuwa na asibitin.

Ministar lafiya ta Ghana, Sherry Ayittey ta ce, zasu dau dukkan matakai na ganin gaskiya dangane da wannan lamari.