Murray ya doke Simon

Hakkin mallakar hoto a
Image caption Murray zai fuskanci Dimitrov nan gaba

A gasar Mexican Open dake gudana zakaran wasan Tennis dan Burtaniya Andy Muray ya kai zagayen kusa dana karshe a karon farko tun gasar Wimbledon a bara

Murray ya doke Gilles Simon da 1-6 7-6 (7-4) 6-2.

Zakaran wasan kwallon Tennis din ya soma wasan sa ne sannu-sannu, amma daga bisani ya mike sosai.

A yanzu Murray zai fuskanci Grigor Dimitrov dan Bulgaria a wasan kusa da na karshe.