Rasha za ta taimakawa Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Soji dubu daya da dari biyar ne suka yi shirin ko ta kwana a Rasha.

A jawabinsa na farko game da abubuwan da ke faruwa a Ukraine, shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci gwamnatin kasar ta hada kai da kasashen Yamma don ceto tattalin arzikin Ukraine.

Sai dai a wani lamari da masu aiko rahotanni ke cewa alamar baki biyu ne daga Moscow, ma'aikatar hulda da kasashen waje ta Rasha na ci gaba da sukar sabuwar gwamnatin Ukraine.

Tun da fari a jiya Alhamis Shugaba Putin ya bada umurnin a yi atisayen soja ba zato ba tsammani a kusa da iyakar Ukraine.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace takwaransa na Rasha Sergei Lavrov ya tabbatar masa da cewa kasarsa ba za ta keta hurumin Ukraine ba,amma Amurka za sanya ido dan ganin matakin da Rashar za ta dauka.

Ya kuma ce a kwanaki masu zuwa Amurka za ta duba matakin da Rasha zata dauka dan tabbatar da wannan batu, domin ganin ko aikinta zai dace da maganar da ta yi.

Karin bayani