Shirin Obama na tallafawa matasa

Shugaban Amurka Barack Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan latin Amurka ne dai suka fi aikata munanan ayyuka a cikin al'uma inji shugaba Obama.

Shugaba Obama ya kaddamar da sabon shiri mai taken ''Naka sai Naka'' domin samar da ayyukan yi ga matasa daga kabilu daban-daban na Amurka.

Mr Obama yace matasa bakar fata da 'yan asalin latin Amurka sun fi aikata munanan aiki a cikin al'umma.

A wani jawabi da ya gabatar mai sosa zuciya, yace alkalumma sun nuna cewa yawancin wadannan mutane rayuwarsu a gidan kaso take karewa, ko kuma su shiga cikin ayyukan ta'addanci, ya kuma ce yana kallon kansa a cikinsu.

Masu aiko da rahotanni sun ce tun fara shugabancin Mr Obama yana gujewa manufofin da suka shafi jinsinsa.

Karin bayani