Shugaba Obama ya sake yiwa Rasha kashedi kan Ukraine

Shugaba Barack Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Shugaba Obama ya yi gargadin cewar za a tilasta wa Amurka da kawayenta su yi amfani da wani mataki mai tsauri muddun dai Rasha ta ci gaba da bin hanyar da ta dauka a halin yanzu a kan Ukraine.

Yana magana ne a fadar Shugaban Amurka ta White House bayan tattaunawa tare da Pirayim Ministan rikon kwarya na Ukraine Arseny

-- wanda ya ce Ukraine ba za ta taba mika wuya ba.

Tun farko Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai gana da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a nan London a ranar Juma'a domin gabatar da wasu jerin shawarwari domin sulhunta rikicin.

Mr Kerry yace sakon Amurka ga Rasha yana nan bai sauya ba.