Majalisar Amurka ta zargi CIA da leken asirinta

Shugabar kwamitin kula da ayyukan leken asiri na majalisar dattijan Amirka Diane Feinstein ta zargi hukumar leken asiri Amirkar CIA da yiwuwar aikata munanan ayyuka leken asiri akan majalisar.

Ta ce hukumar CIA ta binciki naurorin kwamfuta na ma'aikatan majalisar wadanda ke binciken zargin cewa hukumar ta CIA ta azabtar da mutanen da ake tuhuma a zamanin mulkin Bush.

Shugaban hukumar CIA din ya musanta cewa hukumar ta gudanar da aikin leken asiri akan kwamitin.

Kakakin fadar gwamnatin Amirka Jay Carney ya ce, abin da ake zargi an aikata shi ne kafin Obama ya zama shugaban kasa.

Ya ce,"ana magana ne a kan binciken al'amuran da suka wakana karkashin gwamnatin da ta shude wanda tun a wancan lokaci Obama a matsayin dan takara ya yi tir da shi ya kuma yi alkawarin kawo karshensa."