'Jiragen soji sun kashe mutane a Borno'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rohotanni daga arewacin Najeriya sun ce wani hari da jiragen sojin kasar suka kai ya hallaka mutane a wani kauye a Jihar Borno.

Mazauna yankin sun shaidawa BBC cewa a daren jiya ne wani jirgin sama ya saki bam akan garin.

Sai dai Rundunar sojin kasar bata ce komai ba akan lamarin.

Dama dai rundunar sojin saman kasar ta fidda wata sanarwa a jiya dake cewa zata fara kai hare-hare ta sama a yunkurin murkushe 'yan Boko Haram.