An kashe mutane da dama a Maiduguri

Rahotani daga Maiduguri a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya sun ce mutane da dama ne suka hallaka yayinda wasu sun ji raunuka lokacinda wasu bama bamai da aka dana a motar itace suka fashe a unguwar Gomari-binta suga.

Rahotanin sun ce bama-baman da suka tashi sun haddasa gobara wadda ta kona shaguna da kuma gidaje da dama.

Wasu mazauna unguwar ta gomari sun ce sun kai gawawwaki akala hamsin zuwa asibiti, sai dai kawo yanzu jamian tsaro basu ce komai ba.

Tun a watan Mayu na shekarar data gabata ne aka kafa dokar ta baci a jihohin Borno, Adamawa da Yobe domin murkushe ayuikan masu tada kayar baya da ake kira boko haram.

Sai dai kawo yanzu dokar ta bacin ba ta tasiri yayinda mayakan kungiyar boko haram ke ci gaba da kai hare hare.