Borno: Jirgin sama ya saki bam a Daglun

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Jihar Borno ta dade tana fama da rikicin Boko Haram

Rahotanni daga yankin arewa masu gabashin Najeriya sun ce mutane kusan 20 suka mutu, kuma yawancin su tsofaffai, bayan wani harin da aka kai ta sama akan garin Daglun da ke karamar hukumar Askira Uba a jahar Borno.

Mazauna yankin sun shaidawa BBC cewa a daren jiya ne wani jirgin sama ya saki bam akan garin.

Daga cikin wadanda su ka rauni da dama na assibitin garin Mubi da ke jahar Adamawa mai makwabtaka da jahar ta Borno

Sai dai Rundunar sojin kasar bata ce komai ba akan harin.

lamarin kai hare-hare dai ya yi kamari yanzu haka a cikin wannan yanki na kasar Najeriya.