Putin na son a tura dakaru a Crimea

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaba Putin ya bukaci babbar majalisar dokokin Rasha ta amince a tura dakarun kasar zuwa Ukraine.

Bukatar ta biyo bayan rokon da sabon Firaministan Crimea, Sergey Askyonov, ya yi na cewa Rashan ta taimaka masu domin "tabbatar da zaman lafiya" a yankin.

Hukumomin Ukraine sun ce Russia ta tura dakaru dubu shidda a yankin Crimea. Jami'an Ukraine din sun zargi Rasha da takalar fada.

Akwai alamar cewa filaye jirgin sama ukku na Crimean na karkashin ikon Rashan a yanzu, koda yake dai hukumomi a Moscow sun musunta hakan.

Tunda farko dai sabon firaministan Crimean ya roki Rashan data taimaka ma yankin nasa.

Mr Askyonov yace: "Ina rokon Shugaban Tarayyar Rasha Vladimir Putin ya taimaka mana wajen tabbatar da zaman lafiya da kare mutuncin Tarayya Crimea Mai cin gashin-kanta".

A can birnin Donetsk dake kudancin Ukraine dimma, dubban magoya bayan Rasha sun yi wani babban gangami a dandalin birnin.

Su na zanga-zanga ne dauke da tutocin Rashan, su na bayyana goyon bayansu ga abinda suka kira kudurin Crimean na neman hadewa da Rasha.

Birnin Donetsk dai shine cibiyar masana'atun kasar Ukraine, kuma nan ne jam'iayyar shugaban da aka hambarar ne din, Viktor Yanukovych, ke da karfi sosai.

Karin bayani