"Gawa" ta farfado a Amurka

Image caption Walter Williams na murna da ajalinsa bai sauka ba.

Wani mutum da ya yi dogon suma a jihar Mississipi ta Amurka ya firgita ma su wankan gawa bayan da ya farfado a gadon wanka.

Likita ne dai ya tabbatar da mutuwar Walter Williams bayan da zuciyarsa ta daina bugawa.

Sai dai yanzu ya ce duk yadda aka yi na'urar da ke taimaka wa zuciyarsa wurin bugawar ce ta dakata kafin daga bisani ta ci gaba.

Mr Williams, mai shekaru 78 na ci gaba da samun kulawa daga jami'an kiwon lafiya.

Iyalinsa sun ce ya yi matukar farin ciki da ajalinsa bai sauka ba.