Yunwa a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi akan matsalar rashin abinci a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya , bayan kusan shekara guda da barkewar tashe-tsahen hankula masu nasaba da kabilanci da kuma adini a kasar.

Shugaban ofishin Majalisar a kasar , Abdou Deing ya shaidawa kamfanin dilancin labaru na AFP cewa yanayin wahala da mutane ke ciki ya kara munana kuma muddin ba a dauki mataki ba jama'a zasu mutu sakamakon yunwa.

Mr Abdou ya ce da dama daga cikin mutane a kasar na fargabar komawa gida.

Haka kuma manoma basu samu damar aikewa da amfani gonasu ba zuwa sassan kasar kuma wadanda aka rabawa iri kan ci su saboda bakin talauci.