Kungiyar G8 ta dakatar da babban taronta a kasar Rasha

  • 3 Maris 2014
Kungiyar g 8
Kungiyar g 8

Kungiyar kasashe 8 masu karfin masana'antu a duniya, ta yi allawadai da kakkausar murya da matakin sojin da Rasha ke dauka a Ukraine, da cewa hakan keta haddin kasa ne.

Wata sanarwa ta hadin guiwa wadda kungiyar kasashen Turai ta EU ita ma ta sanya wa hannu, ta bukaci Rasha da ta yi kokarin magance duk wata damuwa da take da ita a Ukraine ta hanyar tattaunawa kai tsaye.

Kungiyar ta G 7, ta ce tana dakatar da shirye shiryen babban taron da za ta yi a Rasha a watan Yuni saboda matakin na Rasha.

Sanarwar ta zo ne a yayin da sojojin Rasha ke kara rike iko da yankin Crimea, inda Rashan ke cewa ta dauki matakin ne domin kare al'ummarta sakamakon sauyin gwamnati a Kiev