Kungiyar likitoci za ta ci gaba da aiki a Myanmar

Alummar yankin Rakhine Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alummar yankin Rakhine

Bayan kwanaki kalilan da gwamnatin Myanmar ta dakatar da ayuikan kungiyar agaji ta Medicine San frontiers a kasar yanzu haka kungiyar ta samu damar ci gaba da ayuikanta .

Sai dai gwamnatin kasar ta amincewa kungiyar shiga cikin sauran sassan kasar amma ban da jihar Rakhine .

Muhukunatn kasar na zargin kungiyar agajin da goyon bayan musulmi 'yan Rohingya dake jihar.

Wani jamiin gwamnati ya ce kawo yanzu ma'aikatar lafiya na ci gaba da tattaunawa da kungiyar.