Rasha ta saba dokokin duniya - Obama

Hakkin mallakar hoto
Image caption Obama ya gargadi Rasha kan mayar da ita saniyar ware

Shugaba Obama ya ce Rasha ta saba dokokin duniya, kan yadda karara ta keta haddin 'yancin Ukraine, kuma ya bukaci shugaba Putin da ya janye dakarun Rasha su koma sansanoninsu a Crimea.

A wata tattaunawa ta waya ta tsawon minti 90 Mr Putin ya gayawa Mr Obama cewa, Moscow tana da 'yancin kare muradunta idan tashin hankali ya cigaba da yaduwa a gabashin Ukraine da yankin Crimea.

Yayin da shi kuma Mr Obama ya yi gargadin cewa idan halin da ake ciki ya ci gaba, to ba shakka Rasha za ta fuskanci hadarin mayar da ita saniyar ware ta fannin siyasa da tattalin arziki.

Shugaban na Amurka ya kuma gayawa takwaran nasa na Rasha cewa duk wata damuwa da Rashan ke da ita kan kabilun Rasha na Ukraine to kamata ya yi ta tattauna batun kai tsaye da gwamnatin Ukraine.