Borno: An kashe mutane 117 a kwana 3

Image caption An kashe mutane da dama a Konduga cikin watannin baya

Ya zuwa yanzu alƙaluma na nuna cewa, daga ranar Juma'ar da ta gabata zuwa Lahadi an kashe mutane akalla 117 a sassan jihar Borno da suka hada da Maiduguri, Daglun, da kuma Mainok.

Harin bama-bamai ta sama da dakarun Nijeriya suka kai garin Daglun da ke karamar hukumar Askira Uba ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20, yawancinsu tsoffi.

Harin wasu bama-bamai a unguwar Bintu Suga a Ngomari a Maiduguri ya yi sandiyyar mutuwar mutane fiye da hamsin.

Harin na Maiduguri an kai shi ne a wani gidan kallon wasan kwallon kafa da a lokacin ya ke cike maƙil da jama'a.

An kuma kai wani harin a garin Mainok dake kusa da Maiduguri ranar Asabar, inda aka kashe mutane 47.

Baya ga kai wannan hari rahotanni na cewa, an kuma ƙona garin na Mainok.

Koda a safiyar yau ma akwai rahotannin dake cewa, an kai wani harin a garin Mafa shi ma a jihar ta Borno.

Ana dai danganta dukkan wadannan hare-hare -ban da na ƙauyen Daglun ga kungiyar Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau, jagoran Boko Haram

Rayuwa cikin fargaba

Jama'a a kusan dukkan sassan jihar Borno na ci gaba da rayuwa cikin rudani, da zullumi.

Wasu daga cikin mutanen da suka kuɓuta daga hare-haren da ake kaiwa a inda aka ayyana dokar ta-baci sun bayyana yadda suke rayuwa cikin fargaba da rashin tabbas.

Yanzu haka dai dokar ta ɓaci na aiki a jihohin Borno, da Yobe da kuma Adamawa.

A 'yan kwanakin nan hare-haren da ake kaiwa a yankin sun ƙaru matuka.

A ƙarshen mako hukumomin tsaron Nijeriya sun ce, suna samun nasara a yakin da 'yan Boko Haram.