Masar ta yi kuskure: inji Fakry

Aljazeera Hakkin mallakar hoto Al Jazeera
Image caption Wakilan Aljazeera da ake tuhuma a Masar

Ministan kasuwanci na kasar Masar ya shaidawa BBC cewa an yi kuskure da aka gurfanar da wasu 'yan jarida na gidan talibijin na Aljazeera gaban kotu bisa zargin taimakawa kungiyar 'yan uwa musulmi.

A hirar da ya yi sashin turanci na BBC Mr Mounir Fakry Abdel Nour, ya yi zargin cewa , yan jaridan, ciki har da tsohon wakilin BBC , Peter Creste na yi wa kafar talabijin aiki wadda ke biyan bukatun kungiyar 'yan ta'ada.

Sai dai ya ce idan yana da zabi da mataki da ban zai dauka a kan lamarin.

Yan jaridan dai sun musanta zargin da ake yi masu