An yiwa Kanu aiki a zuciyarsa

An yi wa ɗan wasan ƙwallon ƙafa na gaba ɗan Nijeriya, Nwankwo Kanu fida a zuciyarsa a wani asibiti a Amurka.

Onyebuchi Abia, shugaban gidauniyar tallafawa masu fama da ciwon zuciya da Nwankwo Kanu ya kafa yace, an yi wa tsohon dan wasan na Arsenal fida ne a karshen mako a wani asibiti da ke Cleveland.

Ya ce, aikin fida ne domin daidaita wata matsala a zuciyarsa.

Onyebuchi Abia ya kara da cewa, dama Nwankwo Kanu ya na zuwa a duba lafiyar zuciyarsa kowacce shekara.

Yanzu haka Nwankwo Kanu ya na murmurewa bayan aikin da aka yi masa.

Cikin shekarun 1990 ne aka yiwa Kanu aiki a zuciyarsa.