Tarzoma a Maiduguri

Image caption Matasa 'yan sintiri a Maiduguri

An yi tarzoma a Maiduguri babban birnin jihar Borno bayan matasan da ake kira 'civilian JTF' sun yi arangama da soja a wani wuri da ake kira Sector 2, kusa da kwalejin koyon aikin gona.

Rahotanni dai na cewa, an kashe mutane

Matasan 'yan gora dake binciken ababan hawa ne suka kama wasu mutane biyar dauke da bidigogi a cikin motar haya sanye da fararen kaya.

Bayan an je ofishin soja an an tabbatar da cewa, mutanen biyar soja ne na gaskiya, an yi harbi lamarin kuma ya jikkata mutane uku.

Su dai matasan sun harzuka ne suna zargin mutanen biyar sojan gona ne.

Matasa da dama sun taru a bakin ofishin sojan, inda aka yi ta kokarin shawo kan sun.

Wannan lamari dai ya tada hankali a wasu sassan birnin na Maiduguri.