'Ba za a murkushe Boko Haram a kwana guda ba'

  • 3 Maris 2014
Minista Abba Moro Image copyright Getty
Image caption Mr Moro ya ce kasashe makwabta na bada hadin kai wajen yaki da Boko Haram

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Abba Moro, ya ce ba zai yiwu a kawo karshen rikicin Boko Haram ba a cikin kwana guda.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake mai da martani ga hare-haren da ake zargin kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad, da wasu ke kira Boko Haram da kaiwa a karshen mako a jihar Borno dake Arewacin Najeriya.

Mutane fiye da casa'in ne dai suka rasa rayukansu a hare-haren, wadanda aka kai kan wasu kauyuka na Jihar ta Borno da ma babban birnin Jihar, Maiduguri inda wasu bama-bamai guda biyu suka tashi a ranar Asabar.

A wata hira da sashen Turanci na BBC, Mista Moro ya kuma bayyana cewa Najeriya na samun cikakken hadin kai daga kasashe makwabta a yakin da take yi da kungiyar ta Boko Haram.

Karin bayani