An fara shari'ar Oscar Pistorius

Oscar Pistorius Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kawun Mr. Pistorius da kanwarsa da kuma dan uwansa sun halarci zaman kotun

Zakaran dan wasan tseren nakasassu, Oscar Pistorius ya musanta zargin kashe budurwarsa Reeva Steenkamp, yayin da aka fara shari'arsa, a Pretoria.

Ana zargin Pistorius da laifin shirya kashe budurwar, bayan ya harbe ta sau hudu da bindiga a watan Fabrairun bara.

Oscar ya bayyana a kotun sanye da bakin kwat, kuma ya wuce mahaifiyar Reeva a zaune, kafin ya kai ga inda kujerarsa take, kuma babu alamun wata damuwa a fuskarsa.

A karon farko a Afrika ta Kudu, za a nuna wani bangare na shari'ar ne kai tsaye.