Fim ɗin da baƙi ya shirya ya lashe Oscars

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Steve McQueen, shi ne ya shirya fim din "Twelve Years a Slave"

Fim din nan na tarihi, mai suna "Twelve Years a Slave" ya lashe lambar yabon nan da ta yi fice ta Oscars saboda ingancin hoton fim din.

Wannan dai shi ne fim na farko da wani baƙi ya shirya ya lashe wannan lambar yabo ta Oscars a wannan mataki.

Steve McQueen dan Birtaniya shi ne ya shirya fim din.

'Yar Kenya, Lupita Nyong'o ce ta lashe lambar yabo ta mai taimakawa jarimin fim da ta fi yin fice.

Chiwetel Ejiofor, shi ne jarimin fim din 'Twelve Years a Slave', wanda asalinsa littafi da wani ya rubuta a kan shekarun da ya shafe a cikin bauta a Amurka.

Asalin Chiwetel Ejiofor dan Nijeriya ne.