'Yan ci rani sun yi zanga-zanga a Saudiyya

Wasu 'yan ci rani daga yankin Asiya a Saudiyya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai 'yan Najeriya takaru da dama a Saudiyya

Rundunar 'yan sanda a kasar Saudi Arabiya ta ce akalla mutum guda ya mutu, bayan wata tarzoma da 'yan ci rani suka yi a inda ake tsare da su.

Yayin da wasu mutane tara kuma suka jikkata, a lokacin da ake turereniya a cibiyar Al-Shumaisi dake kusa da birnin Makka.

Gwamnatin kasar dai ta maida dubban 'yan ci ranin da basu da takardun izini kasashensu, bayan afuwan da aka yi musu ya kare a watan Nuwamba.

A watan jiya ne hukumar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi suka game da halin da ake tsare da wasu 'yan ci ranin.