China za ta dauki matakai masu tsauri a kan tattalin arzikin kasar

Firaministan China Li Keqiang Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firaministan China Li Keqiang

Firaministan China, Li Keqiang ya sheda wa taron shekara shekara na Majalisar Dokokin kasar a Beijin, cewa, har yanzu bunkasar tattalin arzikin kasar shi ne muhimmin abin da gwamnati ta sanya a gaba,.

Sai dai ya ce ana bukatar daukar matakai masu tsauri don cimma hakan.

Mr Li, ya gayawa dubban wakilai a babban zauren taron Majalisar kasar cewa, har yanzu kashi bakwai da rabi cikin dari na bunkasar tattalin arzikin a shekara shi ne gwamnati ta sanya a gaba.

Da yake magana kan matsalar gurbata muhalli, fraiministan ya ce, girgijen hayakin da ya mamaye samaniyar da yawa daga cikin biranen Chinan, gargadi ne na irin abubuwan cigaban da ake yi ba tare da la'akari da illolinsu ba.