An haramta ƙungiyar Hamas a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Field Marshal Al Sisi, Jagoran sojan Masar

Wata kotu a Masar ta haramta dukkanin harkokin ƙungiyar 'yan gwagwarmayar nan ta Palasɗinawa, Hamas.

Kotun ta kuma bayar da umurnin ƙwace ofisoshin ƙungiyar ta Hamas a Masar.

An yanke wannan hukunci ne sakamakon karar da wani lauyan Masar, Sameer Sabry ya shigar.

Mai ƙarar nemi a ayyana Hamas a matsayin kungiyar 'yan ta'adda saboda alakar ta da kungiyar 'yan uwa musulmi ta Masar.

Wani kakakin ƙungiyar Hamas, Sami Abu Zuhri, ya yi Allah wadai da hukuncin kotun, yana mai cewar zai yi illa ga fafutikar Palasɗinawa.