An kashe mutane 11 a harin Jakana

Wani sojin Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Garuruwan dake kewayen jihar Borno sun gamu da karin hare-hare a 'yan kwanakin nan

Akalla mutane 11 ne suka kone kurmus, a harin da ake zargin 'yan kungiyar da aka fi sani da Boko Haram suka kai garin Jakana.

Sanata Khalifa Zannan daga jihar Borno wanda yankin Jakana ke cikin mazabar sa, ya shaida wa BBC cewa, tun a Jiya da yamma mazauna garin na Jakana suka ji labarin maharan sun taru a kusa da garin.

Hakan ya sa duk wadanda za su iya guduwa daga garin suka gudu, aka bar tsofaffi da mata da sauran wadanda ba za a iya gusawa da su ba.

Kuma da maharan suka shiga garin da misalin karfe 8:30 na daren ranar Litinin, sun kone kusan kashi daya bisa uku na garin, amma sojoji sun kai dauki suka fatattaki maharan.