An kori shugabannin ma'aikatun sufurin jiragen sama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Goodluck Jonathan, shugaban Nijeriya

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya sallami shugabannin hukumomin zirga-zirgar jiragen saman kasar, 'yan makonni bayan sallamar minista, Stella Oduah.

Waɗanda korar ta shafa sun haɗa da shugaban hukumar filayen jiragen sama ta ƙasa wato FAAN, George Uriese, da kuma Fola Akinkuotu na hukumar NCAA mai sa ido akan sufurin jiragen sama.

Sun kuma haɗa da Injiniya Nnamdi Udoh shugaban hukumar NAMA mai kula da zirga-zirga a sararin samaniyar Nijeriya, da Chinyere Kalu shugabar makarantar koyar tukin jirgin sama NCAT dake Zaria.

Sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pious Anyim ta kuma sanar da nadin wadanda suka maye gurbin wadanda aka sallama din.

Injiniya Saleh Dumona shi ne sabon shugaban hukumar FAAN mai kula da filayen jiragen sama. Kyafin Muhktar Usman shi ne sabon shugaban hukumar NCAA mai sa ido akan dukkan harkokin sufurin jiragen sama.

Injiniya Ibrahim Abdulsalam shi ne sabon shugaban hukumar NAMA. Kyafin Samuel Akinyele Caulcrick shi ne sabon shugaban makarantar koyar da tuƙin jirgin sama NCAT dake Zaria.

Wannan sauyi a ɓangaren zirga-zirgar jiragen saman na zuwa ne 'yan makonni bayan shugaba Goodluck Jonathan ya sallami ministar sufurin jiragen sama Stella Oduah, wacce ra fuskanci badakalar sayen motoci masu sulke kirar BMW na naira miliyan 225.

Ƙalubale

Ɓangaren sufurin jiragen saman Nijeriya dai na fuskantar kalubale da dama saboda yawan hadarin jiragen sama a kasar.

Koda cikin watan Oktobar bara hadarin jirgin sama ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 a birnin Lagos.

Cikin watan Yunin shekara ta 2012 ma jirgin fasinja na DANA ya halaka mutane 163 a Lagos.

Ana danganta yawan hadurran jiragen sama a Nijeriya ga rashin ingancin sa ido da kuma kiyaye dokoki.