Pistorius: Zaman kotu a rana ta biyu

Oscar Pitorius a kotu a ranar Litinin Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kotun na zamanta ne a birnin Pretoria dake Afrika ta Kudu

Lauyoyi masu kare dan wasan tseren nakasassu, Oscar Pistorius sun ci gaba da yin tambayoyi ga mai bada shaida a rana ta biyu na shari'arsa.

Sai dai an dan dakatar da zaman kotu, bayan babban mai gabatar da kara ya yi korafin cewa, an nuna fuskar mai bada shaidar ba da yardarta ba.

A ranar Litinin makociyar Oscar Michelle Burger, ta shaida wa kotun cewa ta ji kururuwa daga gidan Pistorius, kuma ta ji harbin bindiga.

Hakan a cewarta ya faru ne a ranar da Oscar ya kashe budurwarsa Reeva Steenkamp.

Sai dai Mr. Pistorius ya ce ya kashe budurwarsa ne akan rashin sani, saboda ya dauka wani ne ya shigar masa gida.