Saudi ta hana tallan ababen kara kuzari

Ababen sha masu kara kuzari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Haramcin ya shafi talla ta kowace fuska ta jaridu, mujallu, radiyo ko talabijin

Hukumomin Saudiyya sun hana tallar abubuwan dake kara kuzari, kamar RedBull da sauransu, a wani mataki na kare lafiyar jama'a.

Kamfanonin dake yin abubuwan sha masu kara kuzari, ba za kuma su dauki nauyin kowacce irin dawainiya ba, ko ta wasanni ko al'adu.

Kuma an bukaci kamfanonin su sanya kashedi da Larabci da kuma Turanci a rubuce, a jikin kwalabe ko gwangwanin abubuwan sha dake kara kuzari, domin sanar da illar dake tattare su.

Haka kuma za a haramta sayar da irin wadannan abubuwan sha, a bainar jama'a da makarantu da filayen wasanni.